ASSALAMU alekum yan owa barka da zuwa shafin TANIMU1 TV
yauma kamar kullin munkawomaku wani saban WhatsApp 2.21.10 lite 2021
zaku iya saukewa cikin sauki mungode
DOWNLOADING WHATSAPP LITE 2.21
(1)
TAMBAYA
=========
Assalamu Alaikum Allah ya gafarta malam,Tambayata itace,namijine ya rasu yabar yara biyu mace da namiji,macen shekararta biyu namijin shekarsa hudu akabarsu hannun mahaifiyarsu har zuwa yanzu da namijin yakai shekara cikin ta goma maccen shekara cikin ta bakwai,tun daga lokacinda Allah yakarbi ran mahaifinsu, dangin mahaifin sundauki nauyin yaran babu abunda basu yimusu indai ansanar dasu,to shine yanzu muka bukaci sudawo hannumu saboda mahaifiyarsu tayi aure kuma ba gari guda da yaranba,to shine abun yazama bacin rayuka wai hakan bazai yuyuba tunda mahaifiyar uwar tana raye,to malam muna neman abunda Allah da manzosa sukace akan hakan,da kuma shawara.Allah ya sakawa malam da alkhairi,kuma Allah yasa mudace.
AMSA
======
A yanzu, Sakamakon Mahaifinsu baya Raye. Mahaifiyar Su itace tafi Kowa Girman Hakki wajen daukar Rainon Wadannan yaran.
Sai dai Kuma idan ta bayar da su ya zuwa ga yan uwan Mahaifinsu yayi. Sabida Samun Kulawa ta Dawainiyar Rayuwar su.
Sai dai kasancewar ita din tana son zama da su. To fa Wajibi ne zaku bar mata su. Sai ku ci Gaba da kyautata musu Kamar yadda Kuka Saba a Matsayin su na 'yayanku.
Sabida ba Mamaki Akan ku Rabata da Wadannan Yaran. Zata iya Hakura da zaman wannan Auren da kuke gani.
Matukar dai shi wannan Mijin Nata ba zai tsangwame su ba. Ku bar mata su. Sabida itaCe ta di kowa chanchanta da Rike Su.
Amma da Ace Mahaifinsu yana Raye, kuma basa tare da shi. Ma'ana Sun Rabu. Duk da Haka itace zata Rike Wadannan Yaran Matukar ba tayi Aure ba. Sai Dai kuma, da zarar tayi Aure, to fa Wajibi ne zata bashi 'yayansa Domin ya basu irin Tarbiyyar da ta dace da ta Ubansu. Ba Tarbiyyar gidan wani ba. Wannan Shine Hukuncin da Manzon Allah saw yayi Akan wata Mata da bata tare da Mijinta. Mijinta ya zo zai karbe Dansa. Manzon Allah saw Yace ya bar mata yaron ta, har sai Tayi Aure. Sannan sai ta bashi. Yana nan Cikin Sunan Abin dawud. BABU MAN AHAQQU BIL WILADATI. Ma'ana Babin ds yake Magana akan wanda Yafi chanchanta da kula da Renon Yaro.
Sabida Akasari idan mace ta je da dan wani Mutumin gidan da ba gidansu ba. Ana Samun Matsala. Akan wannan dan ko diyar sai Auren ya Mutu ko kuma shi Mutumin ya kasa Baiwa wannan yaron Tarbiyya, ya bar shi ko ya bar ta babu Kulawa. Sakamakon ba shine ya Haifeshi shi ba.
Wani Lokacin ma idan mace ce. Ana Samun Matsala. Idan Mijin da ta Aura bashi da Tarbiyya. Sai kaga yana Neman ya Afkawa Wannan Yarinyar. Ana Samun irin wannan Matsala.
Sabida haka kenan Matukar wanda kika Aura bashi da wata ingantacciyar Tarbiyya, to fa sai Kina Taka Tsan-tsan da yarinyarki. Wani Kuma zai Rike ne Tsakaninsa da Allah. Wanda Kuma idan yayi hakan. Zai dace Duniya da Lahira.
Haka zalika Ya Kamata Mata Kuna Kai Zuciya Nema. Musamman m ga wadda ta san tana da yara Mata. Wajibi ne sai ana Hakuri. Bacin Rai Kadan Yana Sawa ki tafi ki bar yaranki. a haka sai ana Samun Matsala. Wani Uban Ma sai ka ga shine yake Lalata Diyar da ya Haifa ta Cikinsa. Musamman ma idan aka samu karo da Tarbiyya Gurbatacciya.
Domin Akasarin Kuna Auren Maza ne idan suna da wani Abu. Ba dan Allah ba. Ma'ana ba masu Addini da Tsoron Allah ba. A haka ake ta samu sai ka ga mace Taci karo da Rashin Tarbiyya. Da Wulakanci. Shiyasa Bahaushe yake Cewa idan Da Kwadayi da Wahala.
Sabida haka Mata ya Kamata An Kiyayewa. Sai dai idan baki Kiyaye ba. Zaki zo kina da Na Sani.
Allah Shine Masani.
(2)
CUTAR DANYA/SHAWARA/YELLOW FEVER
Wannan Cuta Ana kiranta da Cutar Danya da yaren Hausa. Da yaren Turanci kuma yellow fever.
Wannan cuta ba sabuwar Cuta Bace. Ta Dade tana Addabar Banu Adam. Musamman ga wanda yake yawwn shan Kayan Maiko
Wanda kuma Daga cikin Gwaje-gwajen da Akeyi Yiwa Duk Wanda Zai shiga Kasar da ba tasa ba, domin tabbatar da lafiyarsa Akwai Gwajin wannan Cuta Ta Danya/yellow fever.
Sannan Kusan Duk Kasar da ka sani, idan Suka tabbatar da kana da wannan cutar a jikin ka, to fa ba zaka shiga Musu Kasarcu ba. Idan kuma Allah yasa kana zaune a wannan kasar. To fa duk lokacin da suka tashi yin wani bincike, Suka tabbatar da cewar kana da wannan jinya, tofa zasu Fitar da kai daga kasarsu.
Wannan jinya tana da Alamomi Kamar haka.
. Maida Kwayar Idon Mutum yayi Kore. Wanda Asalin Idanuwan Mutum Fari ne da kuma bakin tsakiya Kamar yadda kowa ya sani. Amma zai Maida Idanuwan Mutum Su zama Kore-Kore ko wata Rawaya-Rawaya.
. Tafin Hannun Mutum Zaiyi Fari, Kamar babu Jini a jikinsa.
. Wani Lokacin zakaga Cikin Mutum yayi Girma sosai, sabanin Sauran jikinsa.
. ko kuma Yawan Yin Barci. Zakaga Mutum Baya Gajiya da barci, sannan a Koda Yaushe zaike yawan jin barci.
A kasuwa Barci, a wajen Aiki Barci, A gida barci da dai Sauransu.
. Yawan Jin Kasala. Mutum Kullum Sai yake jin jikin sa Kamar yayi wani Aikin Karfi ya Gaji.
. Yawan Yin Zazzabi Akai-Akai.
. yawan yin Amai Mai Daci. Wani Lokacin zaka ganshi Kore.
. Yawan tashin Zuciya.
. Ciwon Ciki Akai-Akai.
. Yawan Zafin Jiki.
Wannan kadan daga Hanyoyin da Ake gane Irin wannan jinya.
Allah yayi mana tsaro da wannan jinya.
Akwai Kuma Maganin INGACCEN HAWAN JINI.
Wanda Yake da irin wannan Jinya, Muna Masa Addu'ar Allah ya bashi Lafiya, sannan kuma idan har Allah yasa mai irin wannan Jinya yaci Karo da Wannan Rubutu kuma ya gamsu, Sannan kuma yana bukatar Magani, Zai iya Tintibarmu a Number Waya
ZAUREN SUNNAH ISLAMIC MEDICINE CENTER
Post a Comment
0Comments