SHU OMA 11

TANIMU1 TV
By -
2

Barka da zuwa shafin TANIMU1 TV 


SUBSCRIBE MY CHANNEL





idan kunji dadin wanga video kutura zuwa wasu group WhatsApp dinku ko Facebook domin kowa ya anfana dashi mungode sosai dakulawa allah barmu tare naku TANIMU1 TV channel
TAMBAYA
========

Assalamu alaikum mlm yafama da jama a Allah yasakawa Malam da alkhairi Ameen mlm Dan Allah shawara nake nema kabani mlm aurnane yamutu watanni wajan takwas yanxu. To seyanxu nafuskanci kuskurena Shima Kuma mijin nawa nafuskanci kuskurenshi Kuma nunaqaunar junammu mun haihu dashi yaronmmu daya to mlm seda nayiwa mahaifiyata magana setacemin ita gaskia bata yaddaba bazan komaba wai nayayemishi dansa nabarmishi danashi dansa naje na auri wani nikuma wllhy mlm inasan mijina duk mutumin da yazomin da niyyar aure wllhy senaji banasanshi se mijina nabaya nakeso to yanxu da nadage wai duk ta kwashe kayan aure nawa wai ko cokalinta bazan daukaba naje na mayar da auran ita babu ruwanta Kuma auran zuminci ne da ita da mahaifiyarsa uwarsu daya ubansu daya to niyanxu narasa yadda zanyi Ni yaron damuka Haifa dashi wllhy shinakeji Dan Allah mlm kabani shawara Dan  Allah mlm ngd.


AMSA
=====

 Na Farko dai, ya Kamata Ita Mahaifiyar Ki Ta Sani Cewar Ba'a yiwa Bazawara Tilas Akan Wanda Zata Aura Ko wanda bata so ta Aura. Itace take da Hakki ta zabarwa Kanta wanda zata Aura.  
  Sabida haka Kenan. Tinda Har Kun Gane Kuskurenku. In har a Tsakanin ne. To ba Lefi Bane Ku Sasanta Junanku. Ki Shirya ki Koma Gidan Mijinki.
  Idan Kuma a Zamantakewarku ya Batawa iyayenki l, Sabida Ana Samun Haka. Sai Kiga Miji ya Wulakanta Surukansa, ya saka Musu Diyarsu. Daga baya Kuma ya dawo ya gane kuskurensa. Idan har haka ne ya faru. To su ki gaya masa ya je ya sameta ya bata Hakuri Akan Abinda yayi Mata na Ba Daidai ba. 
 Abin da Ciwo Gaskiya, Kana Auren diyar Mutum kuma ba wanda ka Rena Irinsa. Wannan ba Daidai bane. Sabida haka idan har ya san yayi Mata ba Daidai ba. Yaje ya Kaskantar da kansa ya bata Hakuri sai kiga ta Hakura. Musamman ma da kika ce Kanwar Mahaifiyar sa ce.
 Idan Kuma ba Haka Bane. Bai Kamata Ta Hanaki Komawa Ba. Domin ba ta da Hakki a Musulunci da zata Iya Hanaki ki Komawa Gidan Mijinki. Allah ne da Kansa ya bayar da wannan damar na Komawa. Kuma Allah ya fi son ma a daidaita a Koma. Shiyasa ma ya gindaya Sharudan idda a gidan Miji. Kun Rabu Jama'a basu Sani ba. Kun Koma Jama'a basu sani ba. In banda Iyayenku. Sannan kuma da Allah Yace ta Zauna tayi idda a Gidanta. Ae dan kana ganinta, ta haka ne zakake Tuno Alkairanta, Harma ka Hakura ka Mayar da Matarka.
 Sabida haka Tinda kowa ya gane Kuskurensa da kuka yi. Harma Kun daidaita Komawa Aurenku. Idan Kuma Anbi duk wata hanya ta Sulhu da ita Mahaifiyar Ki din, taki Yarda Akan Ki Koma Gidan Mijinki. Sai ki Tuntubi Alwalinki kiyi Masa Bayani. Musamman Alwali daga Dangin Mahaifi Yake. Domin Sune suke da Hakkin Daura Miki Aure.
  Amma fa har sai kin tabbatar da Cewar idan kin Koma zaku Zauna zaman Lafiya. Domin idan Wannan Mijin Naki ya dawo da halayensa. Har ta kai da Ya sake sakin ki. To fa ki sani ba zaki Koma Gidan Mahaifiyar Ki Ba. Tinda ba ta so kika Koma.
 Kuma duk da haka ba kaurace mata zakiyi ba. Zakike zuwa kina Rarrashin ta. Kina Nuna Mata Cewar Ita Kaddara idan Allah ya Rubutawa Mace Aurenta da wane bai kare ba. Dole dai ana Nan, babu Ranar Rabuwa da Juna. Har Sai Idan Kaddarar Rabuwar Ce ta Zo.
 Sabida inda matsalar take. Zaki Iya zama ke bakiyi Auren ba, Kuma baki Koma Gidan Mijinki ba. Domin Hakan tana Faruwa ga Wasu Matan. Ko kuma Baki san Kalar Namijin da zaki sake Aura ba. Amma idan Kina tare da Mijinki zaku samu ku tallafi Tarbiyyar yayan da Allah ya Baku. Wanda a Rashin Samun ingantacciyar Tarbiyya, yaron ku zai Iya Haduwa da Gurbatattun Yara su Lalata Muku Tarbiyyarsa.
  Kuma Ki Lallaba Mijinki Ku Zauna Lafiya. Kowacce Kalar Mace da Kike gani, Akwai Matsala a Tsakanin ta da Mijinta. Amma a haka ake Zaune da dadi ba dadi, zaman yafi Rabuwar.
 Kuma ya Kamata mata Ku dena daukar Abinda Yake Faruwa a Tsakanin ku da Mazajenku kuna Kaiwa gidajen iyayenku. Daga baya Zaku shirya ku daidaita da Mazajenku, Amma kuma iyayenku ba zasu manta ba. Sun Kullaci Wannan Al'amarin a Zuciyarsu.
 Haka Zalika, ya Kamata Yan Uwana Mata Ku Sani Fa, dole ne Zaman Aure sai da Hakuri. Duk wadda Tace ba Zatayi Hakuri a irin wannan zamanin ba. Wallahi ba zata taba sanin dadin Aure ba. Domin a koda yaushe ta dinga Rayuwa a Cikin Zawarci.

YA ALLAH KA ZAUNAR DA AUREN MU LAFIYA. MARASA AURE KUMA, ALLAH KA KAWO MUSU MAZAJE NA GARI, WADANDA ZASU ZAUNA DA SU LAFIYA SU TAUSAYAWA RAYUWARSU.

Allah Shine Masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 

Post a Comment

2Comments

Post a Comment