SABAN WHATSAPP NA 2021 WANDA ZAKU JIDADINSA SOSAI DOMIN YAZODA SANIN ABUBUWA MAMAKI
Aslan alekum yan owa barka da zuwa shafin TANIMU1 TV
idan da abunda baku ganeba zaku iya mana nagana a Comment Comment mungode sosai dakulawa allah barmu tare
TAMBAYA
========
Aslm amincin Allah a gareka ya malam y kk y gd kuma to Allah yasa aljannane mako marka Ameen ya Allah .malam don Allah ina neman shawaranka ne kuma da yaya matsayin abun a musulunci malam nine nakasance nafara son wata yarinyar tun da yarinta kuma ga shi mun girma a she ita tana nan tana sona nima kuma har ga Allah ina sonta malam saide matsala guda daya malam nayi buncike a kanta malam gaskiya nasamu labarin wai anta pa lalata da ita anma kuma ita taki tafadamun to shine na kuma ita tana sona malam to shine nake nemar shawaranka xan iya sonta ko kuma naya hakuri don har ga Allah ina son nayi aure ne shiyasa nake neman shawaranka malam Allah yayi albarka Ameen Nagode.
AMSA
======
Idan ka san wannan Ba zai zama matsala a zamantalewarka da ita ba, zaka Iya Aurenta.
Idan Kuma kasan wannan zai Iya sanadin da zai sa Kake Wulakanta ta ko ka Goranta Mata ko ka cutar da ita ko ka tsane ta daga baya ko kake yawan tayar Mata Da Maganar, To Maganar gaskiya Kar ka sake ka Karbi Soyayyar ta.
Akwai Mutumin da Zaike Yiwa Mace Garin Wani Abu da ya Faru da ita a Rayuwa. Bayan Kuma Wannan Abin Ya Riga da ya Wuce. To idan har kasan ba zaka Iya Hadiye Wannaj Matarsa da ta Faru da Ita ba. to Kar ma ka Fara Neman Auren ta.
Sannan Kuma Wajibi ne ka Rufa Mata Asiri. Kar ka Gayawa kowa. Sabida idan har ka ci gaba da Gayawa Mutane. Ba zata Sami Mijin Aure ba. Kaga Kenan ba ka kyauta ba.
Allah yana son Wanda zai Rufa Wa wani Asiri.
Manzon Allah Saw Yace. DUK WANDA YA RUFA WA WANI ASIRI ANAN DUNIYA. SHIMA ALLAH ZAI RUFA MASA ASIRI A RANAR LAHIRA.
Kaga Kenan Rufawa Bawa Asiri. Ba Karamar Ibada Bace. Domin ba wanda bazai so Allah ya Rufa Masa Asiri a Ranar Lahira ba. Ranar Tonon Asiri. Domin da za'a Tona Asirin wani Ko wata. Wallahi Abin ba zai yi Maka da Dadi ba.
Allah ya Gafarta Mana Gabaki dayan Mu duniya fa Lahira.
Allah Shine Masani.
(2)
TAMBAYA
========
Malam in ina sallah abun inyi karatu kawai sai infara waka ko tunani
Na biyu kuma mijina ne baya sallah sai insa alarm na asuba intadashi amma baya tashi har in gidanmu sai da suka kirashi dinda haka bayayi kuma ga shaye shaye yanzu aurenmu wata uku haryafitamin a Kai wlh
AMSA
=====
Subhanallah Duka wadannan Abubuwa naki akwai Al'ajabi a cikin su. Ma'ana akwai ban Mamaki.
Na farko dai inaga kina da yawan jin wakoki ne yasa har idan kika je sallah Sabida Wannaj Masifar jin Wadannan Wakokin sun Ratsa Zuciyarki. Shiyasa hakan take Faruwa a gareki. Sabida haka kenan. Idan har Haka ne, to fa ya zama Wajibi a gareki Ki dena Sauraron wadannan Wakokin shirmen. Sabida Yawan Sauraron Waka bai Yimiki Rana ba. Asali ma Zai Kai ki ga Halaka. Kina gaban Ubangijinki kina saurarain Waka? Ina jiyr Miki Kar Idan Kinzo Mutuwa ki Mutu kina Yin Waka. Sabida haka Ki Kiyaye Gaskiya.
Manzon Allah saw Yace. Abinda Mutum ya dimantu yana yinsa. Da shi zai Mutu. Kuma da shi za'a ta so shi yana yi a filin Alkiyama.
Ma'ana an sha Samun Mutum ya zo Mutuwa yana Yin Waka. Sabida yadda wadannan Wakokin suka tasirantu da Zuciyarsa.. Wanda kuma Bakinsa ya saba yin Azkar. To zakiga idan Ya zo Mutuwa yana Yin Azkar.
Abu na biyu Kuma. Ke da iyayenki Baku yi Bincike wajen Auren wannan Mijin naki ba. Ko kuma wani Abu Kuka gani da yake da shi yasa kunq ji Kuna Gani kika Aure shi a haka. Sai bayan Aure ne kuma kika ga Abin ba Haka Bane.
Menene Amfanin Zama da dan Shaye-Shaye? Gashi Kuma Wanda ba ya yin Sallah. Subhanallah Subhanallah Subhanallah...
Ma'ana ga shaye-shaye ga kuma Rashin Yin sallah. Menene Amfanin wannan Mutumin a Matsayin Mijin Aure?. A Matsayin Uban yayanki.? Wallahi Indai Mace ta Auri irin Wannan Namijin. Ta Zalunci yayan da ta Haifa. Ba ta Samar musu Uba Na Gari ba. Haka zalika shima Namijin idan har matarsa ta Banza Ce. Ya zalunci yayan da ya Haifa. Sai Allah ya yimusu Hisabi a Ranar Alkiyama.
A shawara ta idan har ba zai ke yin sallah ba. Kuma ba zai Chanza Halinsa ba. Ma'ana idan har ba zai dena yin Shaye-shaye ba. Kawai ya sallameki. Ki je kiyi Addu'ar Allah ya kawo Miki na Gari wanda ba shi ba kuma wanda ba Irinsa ba.
Allah shine masani
Post a Comment
0Comments