(1)
TAMBAYA
=========
Assalamu alaikum wa rahmatullah ta'ala was barkatuhu. Da fatan an tashi lafiya? Dan Allah tambaya ce gareni mlNake so a warwaremin. Mijina baya nan shine qanin mijina yake zuwa ya kwana a gidan da muke Kuma ba wai dakin a waje yake ba irin dakine guda biyu da palour, to shine nake ganin hakan ya sabawa shari'a Dan Yana da inda zai kwana Amma ban San me yasa ya zabi nan din ba. Nayiwa mijina magana Amma shi tsoro yake ji yai magana kar ace ya Kori kaninsa daga gidansa Kuma har ga Allah suna da Wannan dabi'ar Basu damu da zama Babu hijabi ko killace jikinsu a gaban kanin Miji ba, to Ni Kuma nasan ba dadai bane, bana San nima na dau wanna halin. To shine jiya nayima kanin Mijin nawa magana Amma cikin lumana nace Masa Bai Halatta Yana zuwa nan ya kwana ba ko don gudun zargi ma sabida nidin ba wata babba bace sannan Yana da gurin kwana. Bai nuna fushinsa ba Amma sai nake tunanin ko ban kyauta ba. Shine nake son qarin haske. Shin addini ya hallata baligin kanin Miji ya shigo Kuna kwana, Miji Yana nan ko baya nan alhalin Bai rasa wajen kwana ba? Na gode Allah ya bada ikon warwaremin min matsalar. Ya Saaka da alkhairi Amin.
AMSA
======
Hakan da Kika yimasa Nasihance shine Daidai.
Bai Halatta Namiji Ya kwana a dakin Matar da Matarsa ba.
Manzon Allah Saw Yace KU NISANTAR DA NUMFASHIN MACE DA NA NAMIJI. Ma'ana a Nisanci Juna. Sabida Hakan Kusantar Zina Ne. Alhalin Allah Madaukakin Sarki Yace Kada a Kusanci Zina. Wanda na Tabbatar da Ake Ke din May Raunin Zuciya ce. Sai dai wani Labarin Ba wannan Ba.
A Irin wannan zamanin Indai Namiji ya Balaga. Ina ga ba Maslaha bane ya kwana daki da Wata Mace ko da da kanwarsa da suke Uwa daya Uba daya ko Uwa daya ko Uba daya. Asali ma Manzon Allah saw Yace A RABA SHIMFIDAR MAZA IDAN SUKA KAI SHEKARA 10. Bare Kuma Wani Namiji ya Zo ya kwana da dakin Matar Aure. Haka Ae ba Tsari. Ko da Mahaifiyar Sa ce Ae bai Kamata ba.
A Irin Wannan gabar. Wallahi Ansha Samun Matsala Zina ta Ratsa ta Shiga Tsakanin da da Uwarsa, haka zalika ta Shiga Tsakanin Uba da Diyarsa, haka zalika Ta Shiga Tsakanin Kane da Yayarsa, haka Zalika ta Shiga Tsakanin Wa da Kanwarsa. Ba inda Zina Ba ta Ratsa ta Shiga Ba.
Sabida haka a Takaice dai Kinyi Daidai. Kuma Wannan Shine abinda Shari'a ta Nuna. Ma'ana a Nisantar Numfashin da yake Tsakanin Mata da Maza. Shine samun zaman Lafiya.
Kuma da Kikayi Hakan, Kin Kawar da Zargin da Mutane zasuyi Miki da Zai iya Shiga Tsakaninki da shi.
Sannan Ma shi wannan Wanne irin Miji ne kika samu haka.?
Mutane Kala kala kenan.
Allah Shine Masani.
(2)
TAMBAYA
=========
Amincin Allah a gareka y Malam y kk y gd y kokari to Ina rokon Allah yasa aljanna ne makomarka ameen ya Allah Malam don Ina da tambayane malam don Allah maiye hukuncin mai sana.ar dauka photo a musulci kuma wai akwai hadisin da annabi s.w.a yace duk mai dauka photo dan wuta ne to malam don Allah maiye hucin shiwanda yaje a ka daukeshi ngd malam Allah yamaka albarka ameen ya Allah.
AMSA
=====
Na Farko dai, shi Kansa Hoto Haramun ne a Musulunci.
Sabida haka Kenan duk abinda ya zama yinsa a Karan Kansa Haramun ne. To fa Wajibi Sana'a Akansa ma haramun ne.
Manzon Allah saw Yace WANDA YAKE YIN HOTO KO YAKE ZANA HOTO. ZA AYI MASA AZABA A RABAR LAHIRA KUMA ANA CEWA DASHI, SAI KA BUSAWA WANNAN HOTON RAI. Wanda kuma Ba zai Iya Bus Masa Rai ba. Sakamakon Haka Kuma Babu Ranar dena Yimasa Azaba har dai yadda Allah ya so.
Anan ne Ma Babban Sahabin Manzon Allah Saw Abdullahi ibn Mas'ud yake cewa. Idan har ya zama Wajibi sai Mutum ya yi Hoto. Me zai hana yayi hoton abinda babu Rai a tare da shi. Sabida Gujewa wannan Azabar ta Ranar Alkiyama.
Ma'ana sai ya zama Hoton Bishiya ko hoton Gida ko wani Abu na daban wanda babu Rai a Jikinsa.
Amma Kawai Mutum ya Rungumi Fulawa a dauke shi a Hoto. Ko ya Dauki Tattara iyalansa a dauke su a Hoto ya zo ya Lika a falo ko wani guri na daban. Wannan bai Kamata ba.
Sannan Kuma Manzon Allah saw Yace MALA'IKUN RAHAMA BA SA SHIGA GIDAN DA YAKE DA HOTO.
Wannan Ma Ba Karamar Musufa Bace. Ace an wayi Gari. Mala'ikun Rahama ba zasu Shiga Cikin gidan Musulmi ba. To Idan kazo Mutuwa waje zai karfafeka da cikawa da Kalmar Shahada? Alhalin Kuma Kaine ka Janyo Wa Kanka Hakan.
Sabida haka Kenan. Bai Kamata ace an sami Musulmi yana Sana'a Akan abinda Allah da Manzon sa suka yi Hani Akai ba. Kamata yayi ya kama wata Sana'a. Ga sana'o'i nan Kala kala wanda ake Samun kudi a cikinsu, Harma Kuma Ayi Arziki.
Sai dai Malamai Suna Ganin babu lefi yin Hoto na passport ko scanning ko x-ray. Ko kuma daukar Hoton wani Mai Lefi Domin a gano inda yake. Ko kuma daukar Hoton Wani da ya Mutu. Shima don a gano inda Yan Uwansa Suke. Sabida wadannan sun Zama Babin Larura a Rayuwar Dan Adam.
Allah shine Masani.
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797
mungudi
ReplyDelete