idan kunji dadin wanga video kutura zuwa wasu group WhatsApp dinku ko Facebook domin kowa ya anfana dashi mungode sosai dakulawa allah barmu tare naku TANIMU1 TV channel
(1)
TAMBAYA
=========
Assalamu alaikum
mlm tmbyta itace,wata baiwar Allah ce Aljannu suka dameta tun da aurenta gashi auren an kai shekaru da mutuwarsa, tana gida to mlm kullum sai sun jefar da ita wani lokacin tayi fitsari wani lokacin kuma sai dai yawu gata da ibada har azumin nan tana yi. to amman mlm idan suka jefar da ita kafin ta dawo hayyacinta sai tayi ta shan ruwa idan kuma ta dawo hayyacinta akace taci abinci sai tace tana azumi. Idan aka mata ae kin sha ruwa. tace bata sha ba to mlm ya matsayin Azumin ta yake? mlm ayi mana bayani yadda zamu gane Allah ya sakawa mlm da alkhairi.
AMSA
=====
Azumin ta yana nan.
Matsayin ta kamar wadda ta sha Abin sha ne ko ta ci abinci ne Alhalin Kuma tana yin Azumi a Bisa Mantuwa.
Hadisi Sahihi. Manzon Allah shine Yace ALLAH YA DAUKEWA AL'UMMAR SA LEFIN ABINDA SUKA AIKATA A BISA MANTUWA DA WANDA AKA TARSASA SU A BISA TILAS SUKA AIKATA DA KUMA WANDA SUKA YI A. BISA KUSKURE.
Kaga kenan anan sai Mu dauka akan cewar an tursasa ta ne. Domin aljanun da suke jikinta ne suka tursasa ta take Aikata Wannan abubuwa. Harma da Ruwan da take sha. Asalima ba ta san tana Aikata wannan Abin ba. Ma'ana ba ta ma san tana shan wannan ruwan ba. Kuma akwai Yiwuwar wannan Ruwan ba Cikinta ya shiga ba. Cikin wannan Aljanin ya shiga.
Duba da wadannan dalilai da wadansu daban. Babu Abinda ya Shafi Azumin Wannan Matar.
Kuma irin wadannan Aljanu suna da hadari. Domin sukan Fitar da Mutum daga duk wata hanya ta biyayya ga Allah. Sabida Suna kaiwa ga hana Mutum sallah, sukan hana Mutum karanta Alqur'ani, Sukan sanya Mutum yake ayyana sabo Kala kala a Zuciyarsa. Da dai Sauransu.
Amma dai Muna da maganin su insha Allah. Duba da bincike akan Magungunan Musulunci.
Allah shine Masani.
(2)
TAMBAYA
========
Assalamualaikum malam
Gatambayata
Malam dn Allah menene hukuncin matar auran da takeyin zinah
Kuma a shimfidar da suke kwana da mijinta?
Dan Allah malam adaure abani amsa domin wata qawatace.
Kuma wllhy Tana cikin danasani d ladama.
Kuma yawanci tacemin harga Allah mijintane yake jefata acikin wannan halin.
Domin baya Kashe Mata matsalar gabanta.
Ma'ana Koda hidima tatasomata to bayako sauraranta balle ko kwatatta Mata wani abun yyi .
Kamar irrin sha'nin gdnsu ko sha'nin kawaye malam kasan.
Ana anko Amma Koda ankon gdansu bayamata Kuma Koda kwandalah.
Bebata yce takai tace gudummawar Tani hkn baya Mata Dadi.
Shyasa takeyin haka Amma tacemin in Sha allahu tayi ladama bazata sakeba.
Shne nace dn Allah malam ataimaka.
Aganar d ita abinda zatayi Allah y gafarta Mata.
Ma assalam ngd malam.
AMSA
=====
Wannan Iskanci ne gaskiya. Ba ta da wata Hujja Kwakwkwara da zata kai ta ga Aikawa Zina. Kawai dai Yar Iska ce. Kuma ta ji Tsoron Haduwarta da Ubangiji. Dan ma ta ce ta dena.
Akan wani Anko ne Zatayi Zina. Ankon dole ne.? idan ba tayi Anko ba Auren ba zai yiwu ba ko yaya?
Dole ne sai ya bata kudin da za tana kaiwa Kawayenta.? Ina Ruwansa ds kawayenta.?
Kawai dai Yar Iska Ce.
Allah ya shiryar da Mu Gabaki daya.
Allah shine Masani.
Ka dage ka Mori ibadu da ake yi a wadannan darare na goman karshen WATAN RAMADAN. Musamman Ma Sallar TAHAJJUD...
Post a Comment
0Comments