idan kunji dadin wanga video kutura zuwa wasu group WhatsApp dinku ko Facebook domin kowa ya anfana dashi mungode sosai dakulawa allah barmu tare naku TANIMU1 TV channel
TAMBAYA
========
Aslm.
Malam antashi lapia?
Allah yataimaka
Shin malam ya halatta mace tayi planning saboda karatunta ko kuma saboda gudun talauci
Sai tambaya nabiyu mal shin dagaskene inhar mace nada ciki ana goge mata xunubanta harta haihu?
AMSA
======
Na farko dai ya Kamata Kowanne Musulmi ya yarda da cewar Allah Shine yake bayar da Haihuwa yadda ya So. Kamar yadda Kowa ya sani Cewar Allah Ya Baiwa wani, wani kuma ya hana shi. Wani kuma ya bashi Haihuwar 'yaya mata Gabaki daya, wani Maza Gabaki daya, wani kuma a hada masa Maza da mata. Duk wannan ba iyawar Mutum Bace. Fache Kaddarar sa.
Sabida haka komi yana Rayuwa ne bisa tafarkin Kaddarar sa da Allah ya Kaddara Masa. Ba wanda ya isa ya Chanja wannan Kaddarar, Kamar yadda Hadisin Ibn Abbas ya Nuna da kuma Ayoyin Alqur'ani Mavanbanta. Kai in banda Kaddara. In banda Kaddarar Allah. Budurwa ko bazawarar da bata da Aure ko kuma Karuwa da take yawon Banza. Ba zasu taba yarda su Haihu ba. Sabida Gudun Abin Kunya. Amma da yake Kaddarar Allah ta Gabaci Tunaninsu da Shikimarsu da Wayonsu. Zaka ga sai wannan yaron ko wannan Yarinyar ta zo duniya.
Sabida haka kenan Family Planning Baya Hana Haihuwa. Domin nayi Interview da yawa daga ciki Dalibaina mata. Wanda suka Tabbatar Min da Cewar suna yin family Planning, Amma kuma wannan bai hana su Haihuwa ba. Kamar yadda kuma Duk inda ka kai da son haihwar ba ka isa ka Baiwa kanka Wannan Haihuwar ba sai Abinda Allah ya Kaddara maka. Sabida haka kenan babu Wayo Ko dabara da ya isa ya chanja Kaddarar Ubangiji akan Bawansa.
Sai dai na yarda da Mutum ya ce Min. Duk Wanda Allah yasa ba zai Haihu ba. Shine yake da tunanin yin family Planning. Wanda kuma Allah yasa zai Haihu. Matar da Mijin. Sai kaga Allah ya sanya Musu Tsananin Son Wannan Haihuwar.
Ya Tabbata a Zamanin Manzon Allah saw. Sahabbai Suna Yin Family Planning, wanda shi Ake Cewa AZALU (Idan Mutum yana Saduwa da iyalinsa. Lokacin da zaiyi Releasing, sai ya cire Azzakarinsa Ya zubar da wannan Spam din a waje) Kamar yadda Jabir dan Abdullahi ya Ambata. Yace Alqur'ani yana Sauka. Amma ba'a hana mu yin Azalu ba. Da Labari ya zo wajen Manzon Allah saw Akan Suna Yin Wannan Azalu din. Sai Yace da su. "YAYA ZAKUYI DA KADDARAR DA ALLAH YA KADDARA KU? Ma'ana yaya zasuyi da Rubutun da Allah yayi Musu Na Abinda zasu Haifa a duniya tin suna Cikin Mahaifiyar Su?
Duk da Wannan. A Musulunci Akwai Sharuda Wanda idan Mata ko Miji. Zasuyi Family Planning. Wajibi ne ya zama Da Izinin Kowanne daga Cikin su. Ma'ana dole Wannan Matar idan Zatayi Family Planning ta sanar da Mijin ta kuma ta Saurari Izinin sa. Domin yana da Hakki. Haka shima Wajibi ne ya Nemi Izinin ta.
Sabida Yana Faruwa, ba Mamaki tana son Haihuwa. Ko shi yana son Haihuwa. Amma kuma an toshe masa hikimar da ta yayi wannan Auren. Duk da Cewar ba wanda ya isa ya Chanja Kaddarar da Allah ya dora shi Akanta.
Allah shine Masani.
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA
Post a Comment
0Comments