MAKIRI EPISODES 29

TANIMU1 TV
By -
1

 ASSALAMU alekum yan owa barka da zuwa shafin TANIMU1 TV

SUBSCRIBE my  channel 


zaku iya samun cigaba wanga video a wanga APPLICATIONS din 


mungode sosai dakulawa allah barmu tare naku TANIMU1 TV channel 

(1)

TAMBAYA

========


Assalamu akaikum malam barka da safiya malam shin ya halatta miji in yana neman aure ya dinga kiran budurwar da asuba don tashinta a cikin gidan matarsa.


AMSA

=====


Gaskiya Bai Halatta ba. Asali ma Wannan cin fuskar ta gidan ce. Ma'ana cin Fuskar Matarsa Ce.

 Sannan a hakan da yake ganin ba wani Abu bane. zai hada gaba da Kiyayya Tsakanin Wannan Matar da Matar da take waje tin kafin ma ta samu ta Shigo cikin Gidansa Gidansa. Kuma fitinar Kansa zata Dawo. Sabida shine Kullum zaike Raniyar fada. Domin babu zaman Lafiya a Gidansa.

 Wani Irin Wulakanci ne wannan Kana tare da matarka ba ka tasheta sallah ba. Sai wata budurwarka zaka tasa ta tashi tayi Sallah!!! Alhalin tana tare da Iyayenta a gidansu. Ga Wadda Hakkin addininta yake kanka. Ba ka sauke ba zakake tashin wata tayi sallah da Asubahi.  Wannan ba Daidai bane gaskiya.

 Sannan ya Kamata ta sani cewar Wannan abinda ka yi mata. Itama haka zaka yi Mata.

  Sabida haka ya kamata wannan Mijin ya sake salo. Ma'ana ya dena Irin wannan. Cin Fuska ne kuma Wualanta ta gidan ne. Da Nuna cewar ita ba komi Bace.


Allah shine Masani.


(2)

TAMBAYA

========


Aslm malm, tambayata anan shine ni da mijina ne babu jituwa ko nakadan ni Kuma abin nadamuna narasa yanda zanyi da raina inason aure saidai abin nason yafi karfina wanda gani nake nabar gidan kawai, dan Allah mom kabani shawara shekaramu goma Sha daya da aure amma babu dadi a tsakanin mu

Ban rasa Sha ba Kuma ban rasa ci ba

Amma zamantakewan aure babu.


AMSA

======


To menenen damuwar?

 Zaki fara duba Menene Matsalar da ta sa baki da jituwa a Tsakanin Ki da shi din. Duk da ma Mu baki Ambata mana ita Wannan damuwar ba. 

 Amma dai zaki Kalli matsalar. Idan daga wajen ki ne. Sai ki san yadda zaki gyara. Idan kuma daga wajen sa ne. Sai ki bashi shawarwari ta hanyar Amfani da Lafuza Masu dadin Sauraro. Ma'ana ta yadda zai saurareki kuma ya Fahimceki.

 Inaga idan kinbi wannan shawarar insha Allahu zaku sami daidaito a Tsakanin ku. Kuma zamanku zai chanja Zane.


Allah shine Masani.



ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 



Kada ka yi Kasa a Gwiwa Wajen Bautawa Allah (Tsayuwar Dare) a Wannan Gomar karshe Na WATAN RAMADAN.

Post a Comment

1Comments

Post a Comment